News
NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2025
Hukumar Shirya Jarrabawa ta Ƙasa (NECO) ta sanar da sakin sakamakon jarrabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2025, inda kashi 60.26 cikin ɗari na ɗaliban da suka rubuta jarrabawar suka samu darussa biyar da suka haɗa da Ingilishi da Lissafi.
Magatakarda kuma Shugaban hukumar, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Minna, babban birnin Jihar Neja,
Saudiyya Ta Saki ‘Yan Najeriya Uku Da Aka Tsare Bisa Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
A cewar Farfesa Wushishi, adadin ɗalibai 818,492, wanda ya kai kashi 60.26 cikin ɗari, ne suka samu sakamako mai kyau da darussa biyar da suka haɗa da Ingilishi da Lissafi.
Haka kuma ya bayyana cewa, ɗalibai 1,367,210 ne suka yi rijista da hukumar domin jarrabawar, inda maza suka kai 685,514 yayin da mata suka kai 681,696. Daga cikin waɗanda suka yi rijistar kuwa, ɗalibai 1,358,339 ne suka zauna jarrabawar, inda maza suka kasance 680,292 yayin da mata suka kasance 678,047.
