Connect with us

News

Saudiyya Ta Saki ‘Yan Najeriya Uku Da Aka Tsare Bisa Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi

Published

on

WhatsApp Image 2025 09 17 at 11.24.51 750x430

Hukumomin Saudiyya sun saki wasu ’yan Najeriya uku da aka tsare tsawon kusan wata ɗaya a Jeddah bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

wannan na cikin sanarwar da daraktan yaɗa labaran hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), Femi Babafemi, ya fitar ranar Laraba, 17 ga Satumba, 2025.

Saudiyya Ta Saki ‘Yan Najeriya Uku Da Aka Tsare Bisa Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi

Sanarwar ta bayyana cewa waɗanda aka saki sun haɗa da Maryam Hussain Abdullahi, Abdullahi Bahijja Aminu da Abdulhamid Saddieq.

 

Rahotanni sun nuna cewa wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano (MAKIA) ne suka ɗora sunayen mutanen a kan jakunkunan da aka yi amfani da su wajen safarar ƙwayoyi, abin da ya jawo aka kama su a Saudiyya bayan isarsu don aikin Umrah.

 

Advertisement

Binciken NDLEA ya kai ga cafke wani ƙasurgumin ɗan safarar miyagun ƙwayoyi, Mohammed Ali Abubakar wanda aka fi sani da Bello Karama, tare da wasu mutane uku da suka haɗa da Celestina Emmanuel Yayock, Abdulbasit Adamu Sagagi da Jazuli Kabir.

Tuni aka gurfanar da su a kotu.

 

Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (rtd), ya ce sakamakon binciken da suka gabatar tare da shaidun da aka mika ne ya tabbatar da cewa waɗannan ’yan Najeriya ba su da laifi, abin da ya taimaka wajen samun yardar hukumomin Saudiyya su sako su.

Ya kuma gode wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da sauran jami’an gwamnati da suka taimaka wajen tabbatar da cewa ba a zalunci ’yan Najeriya a ƙasashen waje.

 

Advertisement

SOLACEBASE

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending