News
FRSC Ta Tura Ƙarin Jami’ai Kan Hanyar Abuja–Lokoja Bayan Cunkoson Motoci Na Kwanaki Biyu
Hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura ta ƙasa FRSC ta tura ƙarin jami ai a babban titin Abuja zuwa Lokoja don saukaka cunkoson ababen hawa bayan da a ka samu cunkoso tsawon kwana biyu.
Matafiyan a kan titin da ya haɗa da arewaci da kudancin ƙasar sun maƙale a titin har tsawon kwanaki biyu saboda rashin kyan hanya da kuma ƙarin yawan tafiye-tafiye da a ke samu sakamakon karshen shekara.
An Cafke Wata Mata Bisa Zargin Shirya Sace Kanta Tare Da Karɓar Kuɗin Fansa Daga Hannun Mijinta.
Wani daga cikin matafiyan ya ce lalacewar titin da kuma rashin haƙurin masu ababen hawan ne ya janyo toshewar hanyar.
Tsaikon da ya dauki tsawon sa’o’i 48 ya fi tsanani a hanyar Katon Ƙarfe da ya janyo tsaiko ga matafiya.
Kazalika akwai rahotanni da su ka bayyana cewar wasu manyan motoci ne biyu su ka faɗi su ka toshe hanyar titin da su ka ta azzara cunkoson hanyar matafiyan.
Don tabbatar da an warware cunkoson kan titin shugaban hukumar Shehu Muhammad ya ba da umarnin tura ƙarin jami’an.
Kuma ya yi kira ga masu ababen hawan da matafiya da su baiwa jami an hukumar haɗin kai wajen warware matsalar.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
