Connect with us

News

Abin Da Ya Haddasa Hatsarin Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar  ’Yan Wasan Kano – Inji FRSC

Published

on

FRSC

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutum 21 sakamakon mummunan hatsarin mota da ya afku a jihar Kano, inda aka bayyana cewa motar ta dauke da ‘yan wasan da suka wakilci jihar a gasar wasannin motsa jiki ta kasa da aka gudanar a jihar Ogun.

Mai magana da yawun hukumar, Olusegun Ogungbemide, ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne sakamakon gudun wuce sa’a da direban motar ya yi.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Shigar Da Malaman Makarantar Tsangaya 18,670 Cikin Makarantun Boko

Sanarwar ta bayyana cewa motar na dauke da mutane 24, ciki har da maza 23 da mace guda. Cikin mutane 24 din, mutum 21 ne suka rasa rayukansu, yayin da mutum uku – maza biyu da mace guda – suka yi rai .

“An gaggauta kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa daga jami’an lafiya,” in ji Ogungbemide.

Advertisement

Shugaban hukumar FRSC na kasa, Shehu Muhammad, ya bayyana matukar damuwarsa dangane da wannan ibtila’i, tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma gwamnatin jihar Kano.

FRSC ta kuma sake jaddada bukatar masu ababen hawa su kiyaye dokokin hanya, musamman kaucewa gudun wuce sa’a da gajiyawar direbobi yayin dogon tafiya, domin rage yawan asarar rayuka akan tituna.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending