News
Sarkin Jinkan Hausawan Afrika Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Yan Wasan Kano Da Suka Rasu A Hatsarin Mota
Sarkin Jinkan Hausawan Afrika, Ambasada Ibrahim Ali Ibrahim (Abba Alra-iwas), ya bayyana alhininsa dangane da mummunan haɗarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ’yan wasan Jihar Kano 21, a yayin dawowarsu daga gasar wasannin kasa da aka gudanar a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, Ambasada Ibrahim Ali Ibrahim ya bayyana wannan ibtila’in a matsayin babban rashi ba kawai ga Kano ba, har ma da Najeriya baki ɗaya.
Abin Da Ya Haddasa Hatsarin Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar ’Yan Wasan Kano – Inji FRSC
“Lamarin ya faru ne a lokacin da matasan ke kan hanyarsu ta komawa gida domin haɗuwa da iyalansu da abokansu bayan kammala wakiltar jihar a gasar wasannin da ake gudanarwa duk bayan shekaru biyu,” in ji sanarwar.
Sarkin Jinka ya ce abin takaici ne matuka yadda matasa da suka bar gida da ƙoshin lafiya da farin ciki domin hidimar jiharsu, suka gamu da ajali a hanyar komawa gida.
“Abin tausayi ne a rabuwa da masoya a cikin irin wannan hali. Kodayake mutuwa ƙaddara ce da babu wanda zai guje mata, amma yadda aka rasa rayukan matasa masu cike da buri da fata, ya ƙara tsananta zafin wannan rashi,” in ji shi.
Sarkin ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da daukacin al’ummar Kano, yana mai roƙon Allah da Ya jiƙan mamatan, Ya ba iyalansu juriya da hakuri.
Haka kuma, ya yi addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata kuma ke karɓar kulawa a asibitoci, yana mai ƙarfafa jama’a da su dage da addu’a da juriya a wannan lokaci na jimami.
