Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Shigar Da Malaman Makarantar Tsangaya 18,670 Cikin Makarantun Boko

Published

on

Hanya ɗaya tak da za a inganta rayuwar yaran da ke barace barace a Kano da Arewa — Daga Mustapha Hodi Adamu

Gwamnatin Tarayya ta ce ta shigar da malamai 18,670 na makarantun Tsangaya cikin tsarin makarantar zamani, domin a haɗa ilimin addini da na zamani yadda ya kamata.

Shugaban Hukumar Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Kasa (NBAIS), Farfesa Yahuza Imam ne ya bayyana hakan ranar Lahadi a Kaduna, inda ya ce hakan na daga cikin nasarorin da aka cimma a cikin shekaru biyu na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Advertisement

Cutar Zazzabin Lassa Da Bakon Dauro Sun Hallaka Mutum 366 A Jihohi 24 – NCDC

A cewarsa, gwamnatin tarayya ta kafa Shirin Ilimin Almajirai domin rage yawan yaran da ke yawo a titi da bara, tare da ba su damar samun ilimin zamani ba tare da a bar ilimin addini a baya ba.

Farfesa Imam ya ce shirin ya ba da dama sosai, domin yanzu haka yara da malamai a makarantun Tsangaya na samun horo da kayan koyarwa, sannan an hada darussa na sana’o’i da na addini a cikin tsarin ilimi.

Advertisement

Ya ce hukumar NBAIS na aiki a jihohi 29 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.

Haka kuma, ya ce an kaddamar da Qur’anic School Integration Programme (QSIP) domin musamman malamai masu koyarwa a makarantun Tsangaya su samu horo da kuma takardar shaidar makaranta kamar kowane malami.

Advertisement

Ya ce hukumar ta kirkiri jarrabawar Junior Arabic and Islamic Studies Certificate Examination (JAISCE) domin daliban da ke makarantar hadin gwiwa ta addini da boko su rika samun takardar shaidar karatu.

Don tabbatar da haɗin gwiwa, hukumar ta rattaba hannu kan yarjejeniya da manyan cibiyoyi irinsu Nigerian Arabic Language Village Ngala, Jami’ar Fountain a Osun, da Hukumar Tsangaya ta Borno da ta Yobe, da ma wasu daga ƙasashen waje kamar Gambia

Advertisement

 

 

Advertisement

NAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending