News
Cutar Zazzabin Lassa Da Bakon Dauro Sun Hallaka Mutum 366 A Jihohi 24 – NCDC
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta bayyana cewa cututtuka biyu masu hadari – wato Zazzabin Lassa da Bakon Dauro (Diphtheria) – sun yi sanadin mutuwar mutum 366 a fadin Najeriya, tsakanin ranar 1 ga Janairu zuwa 18 ga Mayu, 2025.
A cewar rahoton hukumar, an samu zargin kamuwa da zazzabin Lassa har sau 5,118, inda aka tabbatar da 733 daga cikin su sun kamu da cutar. Wannan na faruwa ne a kananan hukumomi 95 da ke jihohi 18 na kasar nan.
NDLEA Ta Bankado Kungiyar Da Ke Amfani Da Mahajjata Wajen Safarar Miyagun Ƙwayoyi A Kano
NCDC ta ce mutum 141 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da zazzabin Lassa. A mako na 20 kacal na shekarar 2025, an samu karin mutane daga uku zuwa 13 da suka kamu da cutar a jihohin Edo, Ondo da Benuwe.
Rahoton ya kara da cewa adadin mace-macen da zazzabin Lassa ke haddasawa ya karu daga kashi 18.3% a 2024 zuwa 19.2% a 2025, wanda ke nuna cewa mutum daya cikin biyar da suka kamu da cutar na rasa ransa.
Jihohin da cutar ta fi kamari sun hada da Ondo (30%), Bauchi (25%), da Edo (17%), inda su kadai ke dauke da kashi 72% na dukkan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar baki daya.
NCDC ta ce mafi yawan wadanda cutar ke kamawa matasa maza ne masu shekaru 21 zuwa 30, kuma ba a samu rahoton wani jami’in lafiya da ya kamu ko ya mutu ba a lokacin.
Bakon Dauro (Diphtheria) Na Ci Gaba da Yaduwa
A bangaren cutar Bakon Dauro, hukumar ta bayyana cewa daga cikin 2,911 da ake zargin sun kamu da cutar, an tabbatar da 192, yayin da 225 suka mutu sanadiyyar kamuwa da ita.
Yara masu shekaru 5 zuwa 14 ne suka fi fuskantar barazanar cutar, inda maza suka fi yawa da kashi 60% na wadanda suka kamu.
Rahoton ya bayyana cewa cutar ta bayyana a kananan hukumomi 173 a jihohi 24, ciki har da jihohi 10 daga Arewa maso Yamma.
Duk da haka, Kebbi, Katsina, Sokoto da Jigawa ba su cikin jihohin da cutar ta fi yaduwa, inda aka samu kashi 97% na masu cutar daga sauran jihohi.
Domin dakile yaduwar cutar, NCDC ta bude cibiyoyin kula da lafiya da kuma gudanar da taron wayar da kan jama’a dangane da muhimmancin yin rigakafi da kuma sauran hanyoyin kare kai daga kamuwa da cutar.
