News
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
A yau Litinin, 4 ga watan Mayu, 2026, an cika shekaru 24 cif da aukuwar mummunan hatsarin jirgin sama a unguwar Gwammaja da ke birnin Kano—ɗaya daga cikin mafi muni a tarihin sufurin jiragen sama a Najeriya.
Hatsarin ya faru ne a ranar 4 ga Mayu, 2002, lokacin da wani jirgi mai ɗauke da tagwayen inji ƙirar BAC 1-11-500, wanda aka ƙera a ƙasar Birtaniya, ya yi hatsari jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin sama na Kano, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa jihar Legas.
Dr Umar Ardo Zai Maka Jam’iyyar NDC A Gaban Kotu
Rahotanni sun nuna cewa akalla mutane 148 ne suka rasa rayukansu a hatsarin, yayin da wasu 51 suka jikkata. Daga cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su har da Ministan Wasanni na wancan lokaci, Ishaya Mark Aku, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Legas domin kallon wasan sada zumunta tsakanin ƙasashen Najeriya da Kenya.
Kamfanin jirgin, EAS Airlines, ya bayyana cewa mutum huɗu ne kawai suka tsira daga hatsarin, ciki har da fasinjoji uku da kuma ma’aikacin jirgin guda ɗaya.
Masana sun bayyana wannan hatsari a matsayin ɗaya daga cikin mafi muni a tarihin jiragen sama a ƙasar nan, sakamakon yawan asarar rayuka da dukiyoyi da ya haifar.
Lamarin ya kuma haifar da ƙara mai da hankali kan tsaurara matakan tsaro da inganta kula da harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya.
-
News23 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
