News
Duk Da Tsarin Haihuwa Kyauta, Mata Na Ci Gaba Da Biyan Kudi A Wasu Asibitocin Gwamnati A Kano — Rahoto
Duk da cewa gwamnatin Jihar Kano ta bullo da tsarin kula da lafiyar mata masu juna biyu kyauta, wani bincike ya bankado yadda wasu asibitocin gwamnati ke ci gaba da karbar kudade daga iyalan mata masu nakuda, lamarin da ke kara jefa su cikin mawuyacin hali a lokacin da suke bukatar kulawar gaggawa.
SolaceBase ta ruwaito cewa Binciken, wanda ya mayar da hankali kan Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da kuma Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko da ke Gwagwarwa a karamar hukumar Nasarawa, ya gano zargin karbar kudade ba bisa ka’ida ba, tare da tilasta wa iyalai sayen kayan haihuwa duk da cewa tsarin gwamnati ya tanadi wadannan hidimomi kyauta.
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
Gwamnatin jihar ta kirkiro tsarin ne domin rage mace-macen mata da jarirai, tare da saukaka wa iyalai nauyin kudin jinya. Tsarin ya hada da kula da masu juna biyu, haihuwa ta al’ada da ta tiyata, da kuma kula da jarirai.
Sai dai binciken ya nuna cewa a aikace, wasu ma’aikatan lafiya na neman kudi kafin su ba da kulawa, ko kuma su tilasta wa iyalai sayen kayan haihuwa daga wasu wurare.
A cibiyar Gwagwarwa, wasu ‘yan uwan marasa lafiya sun bayyana yadda ake tilasta musu biyan kudin haihuwa kafin a kula da mata masu nakuda. Sun ce kudin na bambanta daga mutum zuwa mutum ba tare da wani tsari a hukumance ba.
Wasu daga cikinsu sun ce idan suka ki biyan kudin, ana iya jinkirta kula da mara lafiya ko kuma a hana su fita daga asibiti bayan haihuwa.
Mariya Hashim ta ce an bukaci ta biya naira 6,500 duk da cewa an shaida musu cewa hidimar kyauta ce.
“Ba a gaya mana dalilin kudin ba, kuma ba mu sayi komai daga asibiti ba,” in ji ta.
Haka kuma A’isha Usman ta ce halin da take ciki bai ba ta damar tambaya ba, domin abin da ta fi so shi ne ceton rayuwar ‘yar uwarta.
Binciken ya kuma bankado zargin hana wasu mata fita daga asibiti har sai sun biya kudin da ake nema.
Ummi Adam ta ce ta shaida wani lamari inda aka tsare wata mata bayan mijinta ya kasa biyan kusan naira 12,000. Duk da ya biya wani bangare na kudin, an ci gaba da rike su a asibitin.
Ita ma Maryam Auwal ta ce an bukaci ta kara biyan naira 100 bayan ta riga ta biya naira 7,000 kafin a ba ta damar ganin mara lafiyarta.
A Asibitin Murtala Muhammad kuwa, binciken ya gano wani tsari da ke nuna yiwuwar hadin gwiwa tsakanin wasu ma’aikatan lafiya da wani shago a wajen asibitin.
Rahotanni sun nuna cewa ana tilasta wa iyalan marasa lafiya sayen kayan haihuwa daga wani shago guda, duk da cewa asibitin na da nasa kantin magani.
Wasu sun ce har ma ma’aikatan lafiya na raka su zuwa shagon, su karbi kudinsu su kai wa mai shagon kafin a ba su kayan.
Wata mata ta ce ta kashe kusan naira 6,500 wajen sayen kayan da ya kamata a samar mata kyauta.
Wasu ‘yan uwa sun bayyana wannan lamari a matsayin cin zarafi ga jama’a a lokacin da suke cikin tsananin damuwa.
Isma’il Muhammad ya ce:
“A irin wannan lokaci, ba za ka iya musu gardama ba. Abin da ka fi so shi ne a taimaka maka cikin gaggawa.”
Sai dai wani ma’aikacin lafiya ya amince cewa ana bukatar marasa lafiya su kawo wasu kayan tsafta, yana mai cewa hakan na taimakawa wajen tsaftar muhalli.
Duk da haka, binciken ya nuna cewa irin wadannan kayayyaki na zuwa asibitocin daga gwamnati, abin da ke kara jefa shakku kan yadda ake sarrafa su.
A baya, gwamnatin Kano ta gargadi ma’aikatan lafiya kan karkatar da kayan asibiti, tare da yin barazanar daukar matakin doka kan duk wanda aka samu da laifi.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce babu wani uzuri na karbar kudi ko tilasta sayen kayan haihuwa, yana mai cewa wasu na kawo cikas ga manufofin gwamnati.
> “Muna samar da duk abin da ake bukata. Abin da ke faruwa ba daidai ba ne,” in ji shi.
Gwamnatin ta dora alhakin kan shugabannin asibitoci, tana mai cewa su ne ke da alhakin tabbatar da bin dokokin tsarin haihuwa kyauta.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin da abin ya shafa ba su fitar da cikakken bayani kan zarge-zargen ba.
Binciken ya nuna cewa akwai gibi mai yawa tsakanin manufofin gwamnati da yadda ake aiwatar da su a kasa. Duk da kyakkyawar manufar tsarin haihuwa kyauta na rage wa jama’a wahala, wasu dabi’u na ma’aikata na ci gaba da jefa iyalai cikin karin nauyi.
