Connect with us

News

Wata Amarya Da Kwarawa Kishiyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Kano

Published

on

Boiling Water

Wata mata amarya ce ta jefa kishiyarta cikin mawuyacin hali bayan da ake zargin ta kwarawa matar tafasasshen ruwan zafi a fuska da jikinta a garin Kumurya da ke Karamar Hukumar Bunkure a Jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya samo asali ne daga wata takaddama da ta kaure tsakanin matan biyu kan amfani da murhun girki, inda sabanin ya rikide zuwa cacar baki da rikici.

Advertisement

GANYEN TAFASA: Ni’imar Allah Mai Tarin Amfani Ga Lafiyar Ɗan Adam

Majiyoyi sun ce yayin da rikicin ke ci gaba, an yi zargin cewa amaryar ta dauki muciya tare da yi wa kishiyarta barazana. Sai dai bayan wasu daga cikin mutanen gidan sun shiga tsakani suka raba su, an ce ta sake dawowa ta debo tafasasshen ruwan zafi tare da kwarawa kishiyarta.

Advertisement

Sakamakon haka, matar ta samu raunuka masu tsanani a fuska da wasu sassan jikinta, lamarin da ya sa aka garzaya da ita asibiti domin ceto rayuwarta.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu, Bello Jibril Gama, mijin matar da abin ya rutsa da ita ya ce har yanzu tana kwance a asibiti tana karbar kulawar likitoci.

Advertisement

A nata bangaren, mahaifiyar matar da aka kona ta ce iyalansu na neman taimakon hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da adalci.

“Abin da muke so shi ne a binciki lamarin yadda ya kamata kuma a tabbatar an karbo wa diyata hakkinta,” in ji ta.

Advertisement

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a samu wata sanarwa daga hukumomin tsaro kan lamarin ba, yayin da al’umma ke jiran matakin da za a dauka bayan binciken da ake sa ran za a gudanar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending