Connect with us

News

Iran Ta Sake Rufe Mashigin Hormuz Bayan Harin Isra’ila A Lebanon

Published

on

images (11)

Iran ta sake rufe mashigin Hormuz a yau Juma’a, maimakon tafiya Switzerland da aka tsara za a tattauna game da yarjejeniyar da Amurka da Tehran suka sanya wa hannu.

Jamhuriyar musulincin ta ce ta yi hakan ne saboda yadda Isra’ila ta ƙi janye dakarunta daga Lebanon, kuma take ci gaba da ƙaddamar hare-hare a kudancin ƙasar.

Advertisement

Wata Amarya Da Kwarawa Kishiyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Kano

Cikin wata sanarwa da aka yaɗa ta kafofin yaɗa labaran Iran, dakarun rundunar juyin juya hali na ƙasar, sun zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita wutar da shugaba Donald Trump da Masoud Pezeshkian suka rattabawa hannu a ranar Laraba.

Advertisement

A cewar rundunar IRGC, cikin muhimman sharuɗa da yarjejeniyar ta ƙunsa har da batun janye dakarun Isra’ila daga Lebanon, da buɗe Hormuz, tare da janyewar dakarun Amurka daga tekun Parisa.

Sanarwar ta ce, tunda dai Amurka da Isra’ila basu mutunta waɗannan muhimman sharuɗa ba, to basu da wani zaɓi face cigaba da rufe mashigin Hormuz.

Advertisement

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending