Connect with us

News

Muna Tantance Yankunan Da Zamu Hana Sana’ar Adaidaita Sahu Da Okada A Abuja ‎ ‎— Wike

Published

on

Wike new 1783596513 768x512

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa gwamnati na duba yiwuwar hana zirga-zirgar baburan Okada da adaidaita sahu a wasu sassan birnin Abuja domin ƙarfafa matakan tsaro.

‎Wike ya ce an cimma wannan matsaya ne bayan taron Kwamitin Tsaron Abuja, inda rahotannin sirri suka nuna cewa masu aikata laifuka na amfani da babura wajen gudanar da wasu ayyukan ta’addanci.

Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutane Biyu, Ta Raba Iyalai Da Muhallansu A Damaturu

‎Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Talata, inda ya ce ya amince da samar da kayan aiki ga jami’an tsaro da  za su yi amfani da su wajen aiwatar da sabon shirin.

‎A cewarsa, ya umarci hukumomin tsaro su tantance yankunan da ya dace a hana zirga-zirgar babura da adaidaita sahu, musamman a tsakiyar birnin Abuja.

‎Sai dai Wike ya ce ba zai yiwu a haramta amfani da su a daukacin Abuja ba, saboda girman birnin da kuma muhimmancin da suke da shi wajen sufuri ga al’umma.

Advertisement

 

PUNCH

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending