Connect with us

News

Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutane Biyu, Ta Raba Iyalai Da Muhallansu A Damaturu

Published

on

1001251098

Akalla mutum biyu sun rasa rayukansu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a birnin Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka yi a ranar Lahadi.

Lamarin ya shafi unguwannin Malari, Pompomari da wasu yankunan da ke makwabtaka da su, inda ambaliyar ta mamaye gidaje da hanyoyi, tare da tilasta wa wasu mazauna barin muhallansu domin tsira.

’Yan Bindiga Sun Sace Tawagar Rakiyar Amarya Daga Katsina Zuwa Kebbi

Rahoton gaggawa da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta fitar ya tabbatar da cewa mutum biyu ne suka mutu a wannan ibtila’i.

Hukumar ta bayyana sunayen mamatan da Isa Haruna, mai shekaru 38 kuma jami’in tsaro, da Abba Kyari mai shekaru 18, wanda ya nutse a yankin Pompomari.

SEMA ta ce tawagarta ta neman ceto ta haɗa kai da jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Yobe bayan samun kiran gaggawa daga al’ummomin da ambaliyar ta shafa.

Advertisement

A cewar hukumar, bayan isa wurin da lamarin ya faru, an tabbatar da rasuwar mutanen biyu, sannan aka kai gawarwakinsu zuwa ɗakin ajiyar gawa na Asibitin Kwararru na Janar Sani Abacha da ke Damaturu.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnatin jihar ba ta bayyana adadin gidaje ko kadarorin da ambaliyar ta lalata ba.

 

 

SAHARA REPORTERS 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending