News
’Yan Bindiga Sun Sace Tawagar Rakiyar Amarya Daga Katsina Zuwa Kebbi
Ana zargin wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matafiya da ke cikin tawagar rakiyar amarya daga garin Sheme da ke Jihar Katsina zuwa Jihar Kebbi, lamarin da ya sake tayar da hankulan jama’a kan matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Rahotanni sun nuna cewa tawagar ta faɗa hannun ’yan bindigar ne yayin da take kan hanyarta ta zuwa Jihar Kebbi domin rakiyar amarya.
Matashiya TV Za Ta Gudanar Da Gasar Masu Ƙananan Sana’o’i A Kano
Mai bibiyar harkokin tsaro a yankin Arewa maso Yamma, Bakatsine, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce an yi garkuwa da wasu daga cikin mutanen da ke cikin tawagar.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da yin addu’a domin Allah Ya kubutar da waɗanda aka sace tare da dawo da su gida cikin ƙoshin lafiya.
Sai dai, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana takamaiman wurin da harin ya faru ba, haka kuma ba a tabbatar da adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba.
Hakazalika, jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba, yayin da har yanzu ba a san halin da waɗanda aka sace ke ciki ba.
-
News6 days ago
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
-
News2 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
