News
Matashiya TV Za Ta Gudanar Da Gasar Masu Ƙananan Sana’o’i A Kano
Gidan talabijin na Matashiya TV ya sanar da shirinsa na gudanar da babbar gasar masu ƙananan sana’o’i a Jihar Kano, a wani ɓangare na bikin cika shekara 10 da kafuwarsa tare da ƙarfafa matasa su rungumi sana’o’in hannu.
Shugaban rukunin kamfanonin Ammasco, Alhaji Mustapha Ado Muhammad, ya bayyana aniyarsa ta bayar da gagarumar gudunmawa domin tabbatar da nasarar gasar.
Tirelar Shanu Ta Kife A Tashar Dukku Da Ke Gombe
A yayin ganawarsa da Shugaban Matashiya TV, Abubakar Murtala Ibrahim, Alhaji Mustapha ya ce matasa su ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma, don haka ya zama wajibi a samar musu da damar bunƙasa sana’o’insu.
Ya bayyana cewa tun da dadewa manufarsa ita ce tallafa wa shirye-shiryen da ke haifar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin matasa.
A cewarsa, ranar gudanar da gasar zai samar da mota mai ɗauke da babban allon majigi domin sauƙaƙa wa mahalarta da baƙi kallon yadda gasar za ta gudana.
Ya ƙara da cewa irin wannan shiri zai ƙara wa masu sana’o’in hannu kwarin gwiwa, tare da jawo hankalin matasa su rungumi sana’a a matsayin hanyar dogaro da kai.
Hakazalika, ya nuna cewa ƙarfafa matasa su shiga sana’o’i na daga cikin hanyoyin rage rashin aikin yi da kuma taimakawa wajen magance matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Matashiya TV ta sanar da cewa har yanzu ana ci gaba da karɓar sunayen masu sha’awar shiga gasar daga sassa daban-daban na Najeriya.
Za a ba waɗanda suka zo na farko zuwa na uku kyaututtuka, yayin da duk mahalarta gasar za su samu takardar shaidar halarta.
Sai dai masu zuwa daga jihohin da ba Kano ba za su ɗauki nauyin zirga-zirgarsu da sauran buƙatunsu da kansu.
Masu sha’awar shiga gasar za su iya tuntuɓar masu shirya ta ta hanyar manhajar WhatsApp domin samun ƙarin bayani da yin rajista.
Za ku iya aikawa da sunanku, adireshi da sana’ar da ku ka ƙware a cikinta a whatsappa https://wa.me/2348096399266
Za a rufe ranar Juma’a 7/8/2026.
-
News6 days ago
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
-
News2 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
