Connect with us

News

Tirelar Shanu Ta Kife A Tashar Dukku Da Ke Gombe

Published

on

IMG 20260804 015142 457

Wata tirela da ke ɗauke da shanu ta kife a shataletalen Tashar Dukku da ke cikin birnin Gombe, lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa tare da jawo taruwar jama’a a wurin.

Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin yayin da motar ke ƙoƙarin wucewa ta shataletalen, inda ta kife, lamarin da ya sa wasu daga cikin shanun suka maƙale a ƙarƙashinta, yayin da wasu kuma suka tsira.

Babu Hidimar Ƙasa Ga Wanda NERD Ba Ta Tantance Ba – NYSC 

Shaidu sun ce jama’ar da ke kusa da wurin sun yi gaggawar kai ɗauki domin ceto shanun tare da taimakawa jami’an da abin ya shafa wajen rage cunkoson ababen hawa da ya biyo bayan hatsarin.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a tabbatar da adadin shanun da suka mutu ko suka jikkata ba. Haka kuma, babu rahoton da ke nuna cewa hatsarin ya yi sanadin mutuwa ko jikkatar wani mutum.

Ana sa ran hukumomin da ke kula da kiyaye haɗurra za su gudanar da bincike domin gano musabbabin aukuwar hatsarin tare da fitar da cikakken bayani kan lamarin.

Advertisement

 

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending