News
AMBALIYA A NEJA: Mutum 110 Sun Mutu, Ruwa Ya Rushe Gidaje Fiye Da 50
Mutane 110 ne suka rasa rayukansu a sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a garin Mokwa da ke Jihar Neja.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (NSEMA) ce ta tabbatar da hakan, inda ta ce ambaliyar ta biyo bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka yi a ranar Laraba.
2026: INEC ta fitar da ranakun zaɓen gwamnonin Ekiti da Osun
Sakamakon ruwan, ruwa ya rusa gidaje fiye da 50, inda wasu suka mutu a nan take, yayin da aka ci gaba da gano gawarwaki a wurare daban-daban a cikin garin.
Jami’an hukumar sun ce har yanzu akwai yiwuwar karin ambaliya, musamman a wasu sassan Mokwa da ke kusa da koguna.
A cewar Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMet), akwai yiwuwar fiye da rabin jihohin Najeriya su fuskanci ambaliya a wannan shekara, saboda tsananin ruwan sama da kuma gurbacewar hanyoyin ruwa.
Hukumomi sun shawarci mutane da su guji zama a wuraren da ruwa ke yawan mamaye, kuma su yi taka-tsantsan domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.
