News
2026: INEC ta fitar da ranakun zaɓen gwamnonin Ekiti da Osun
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da ranar da za a gudanar da zaɓen gwamnonin jihohin Ekiti da Osun a shekarar 2026.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan ranar Juma’a yayin rantsar da sabbin kwamishinonin zaɓe guda shida da Majalisar Dattawa ta tabbatar.
Likitocin Tiyata Kwararru 6 Ne Kacal Suka Rage A Kano – Farfesa Sani
A cewarsa, za a yi zaɓen gwamnan Jihar Ekiti a ranar 20 ga Yuni, 2026, inda zaɓukan fidda gwanin jam’iyyu za su fara tun daga 20 ga Oktoba, 2025. Jam’iyyu za su shigar da bayanan ‘yan takararsu ta shafin musamman na INEC, wanda za a rufe a ranar 22 ga Disamba, 2025.
Za a fara yakin neman zaɓe a jihar a ranar 21 ga Janairu, 2026, wanda zai ƙare kwana ɗaya kafin zaɓe, kamar yadda doka ta tanada.
Ga Jihar Osun kuwa, zaɓukan fidda gwani za su gudana daga 24 ga Nuwamba zuwa 15 ga Disamba, 2025.
INEC za ta buɗe shafin shigar da bayanan ‘yan takara daga jam’iyyu a ranar 9 ga Fabrairu, 2026, kuma za a fara yakin neman zaɓe daga 11 ga Maris, 2026, wanda zai ƙare sa’o’i 24 kafin zaɓe.
Farfesa Yakubu ya kara da cewa INEC na ci gaba da shirye-shirye don gudanar da zaɓukan cike gurbi a kujerun majalisun dokoki na tarayya da na jihohi.
