News
Likitocin Tiyata Kwararru 6 Ne Kacal Suka Rage A Kano – Farfesa Sani
Wani kwararren likitan tiyata, Farfesa Sani Ali Aji, ya ce likitocin tiyata kwararru guda shida (6) ne kacal suka rage a fadin Jihar Kano, duk da yawan jama’arta da ya haura miliyan 20.
Farfesa Sani ya bayyana hakan ne a wani taron kwarewar likitoci da aka gudanar a Kano, inda ya bayyana cewa karancin albashi, rashin kayan aiki na zamani da rashin walwala ga ma’aikatan lafiya ne suka jawo yawancin likitocin kwararru barin kasar domin neman ci gaba a kasashen waje.
Zaɓen Kananan Hukumomi: Gwamnatin Kano Ta Ce Dimokuraɗiyya Ta Yi Nasara
“Yanzu haka yawancin likitoci suna barin kasar nan su nufi Turai da kasashen Larabawa saboda rashin kayan aiki da kuma albashi mara kyau,” inji shi.
Ya ce mafita ita ce gwamnati ta inganta walwalar ma’aikatan lafiya ta hanyar samar da kayan aiki da kuma kara albashi domin jawo hankalin likitoci su zauna a gida.
Farfesan ya bayyana cewa taron da aka saba gudanarwa a kasar Mali, a bana aka gudanar da shi a Kano, inda ya ja hankalin masana da likitoci daga sassa daban-daban na duniya.
