Connect with us

News

Zaɓen Kananan Hukumomi: Gwamnatin Kano Ta Ce Dimokuraɗiyya Ta Yi Nasara

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana farin cikinta da hukuncin da Kotun Daukaka Ƙara da ke Abuja ta yanke, inda ta soke hukuncin Kotun Tarayya da ke Kano.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Oyewumi, ta ce Kotun Tarayya ba ta da hurumin sauraron ƙarar da ke da nasaba da harkokin zaɓen kananan hukumomi, wanda ya saba da tanadin dokar kasa.

Advertisement

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Soke Hukuncin Babbar Kotun Tarayya Kan Zaɓen Kananan Hukumomin Kano

Tun da fari dai, jam’iyyar APC tare da wani bangare da ke ikirarin cewa su ‘yan NNPP ne, sun shigar da ƙara suna zargin cewa shugaban hukumar zaɓe ta jihar, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, bai da adalci wajen gudanar da zaɓen.

Amma a hukuncinta, Kotun Daukaka Ƙarar ta goyi bayan Gwamnatin Kano, inda ta tabbatar da cewa zaɓen da aka gudanar a kananan hukumomi 44 da mazabu 484 a jihar ya kasance bisa doka kuma sahihi.

Advertisement

Gwamnatin Kano ta bayyana hukuncin a matsayin nasarar dimokuraɗiyya da kundin tsarin mulki, tana mai cewa hakan ya nuna cewar shari’a na ci gaba da zama mafaka ga kowa da kowa.

A wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar, ya ce wannan hukunci ya nuna jajircewar Gwamna Abba Kabir Yusuf da hukumar zaɓe ta jihar wajen tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin dimokuraɗiyya.

Advertisement

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa al’ummar Kano bisa juriya da haƙuri da suka nuna yayin da ake jiran sakamakon wannan shari’a.

Kwamishina Waiya ya ƙare da taya Gwamna Abba da al’ummar jihar Kano murna bisa wannan nasarar da ta fito daga kotu, yana mai cewa hakan ya ƙara tabbatar da matsayin jama’a a tsarin mulki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending