Connect with us

News

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Soke Hukuncin Babbar Kotun Tarayya Kan Zaɓen Kananan Hukumomin Kano

Published

on

Abba

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zaune a Abuja ta soke hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke kan hana gudanar da zaɓen kananan hukumomi a jihar Kano.

A baya, jam’iyyar APC tare da wasu masu ƙorafi sun shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya, inda suka nemi a dakatar da zaɓen, suna zargin cewa shugaban hukumar zaɓe ta Kano (KANSIEC) yana da alaka da jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar.

Advertisement

Sojojin Nijeriya Sun Kashe Ƴan Ta’adda 60 A Bita, Jihar Borno

Sai dai yayin da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, mai shari’a Abubakar Babandi Oyewumi ya bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya bata da hurumin sauraron irin wannan ƙara da ta shafi zaɓen ƙananan hukumomi, don haka hukuncin da ta yanke ba shi da inganci.

 

Advertisement

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayyana cewa matakin da Babbar Kotun ta dauka ya saba wa tsarin doka, saboda haka ta amince da bukatar gwamnatin jihar Kano da sauran wadanda suka daukaka ƙara, tare da rushe hukuncin na baya baki ɗaya.

Wannan hukunci na nufin cewa babu wani shinge na doka da zai hana hukumar KANSIEC ci gaba da shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending