News
Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin lagos Daga Rusau Din Gidaje A jihar
Babbar Kotun Jihar Lagos da ke Ikeja ta bayar da umarnin dakatar da Gwamnatin Lagos da hukumominta daga ci gaba da rusau din gidaje a wasu sassan Unguwar Oworonshoki, karamar hukumar Kosofe.
Alkalin kotun, L.A.M. Folami, ya bayar da wannan umarnin wucin gadi ranar Juma’a, 14 ga Nuwamba, 2025, biyo bayan karar da wasu mazauna yankin huɗu suka shigar a madadin Kungiyar Cigaban Al’umma (CDA) da mazauna titunan Olabode Aluko, Iye-Ekiti Close da Church Street.
A cikin karar, an lissafa LASBCA, Mai Martaba Oba Babunde Saliu, da Gwamnatin Lagos a matsayin wadanda ake kara. Kotun ta haramta wa wadanda ake kara da wakilansu shiga.
Dakatarwar za ta tsaya tsawon kwanaki bakwai, yayin da masu kara ke shirin gabatar da cikakkiyar karar. Kotun ta kuma bukaci tabbacin N10m domin diyya ga wadanda ake kara idan aka samu rashin da’a a dakatarwar.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
