News
Cin Abincin Dare Bayan Karfe 9 Na Iya Haifar da Hatsarin kamuwa da Cututtukan Zuciya Da Na Magudanar Jini
Masu bincike a Faransa sun gargadi cewa cin abinci da dare bayan karfe 9 na dare na iya ƙara haɗarin kamuwa da cututtukan zuciya da na magudanar jini.
Masu binciken sun binciki yanayin cin abinci na sa’o’i 24 na misalin mutane dubu 103 a Faransa kuma sun bibiyesu cikin tsawon shekaru 7.2. Matsakaicin shekarun wadannan mutane dubu 103 ya kai kusan 43 a duniya, kuma 79% mata ne. An rubuta matsakaitan yanayin cin abincin 5.7, adadin yanayin cin abincin mafi yawa da aka rubuta kuma ya kai 15. A cikin lokacin da aka bibiyi wadannan mutane, wasu 2,036 sun kamu da cututtukan magudanar jiki a zuciya da kwakwalwa, ciki had da ciwon zuciya da shan inna.
Masu binciken sun gano cewa, wadanda suka ci abincin dare bayan karfe 9 na yamma sun fuskanci hadarin kamuwa da shan inna da sauran cututtukan magudanar jini da 28%, idan aka kwatanta da wadanda suka ci kafin karfe 8 na yamma.
Me ya sa hakan? Madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, hawan jini yana raguwa da dare. Wasu nazarin dabbobi sun nuna cewa, idan an ci abinci a makare, narkewar abinci na iya kara yawan sigar jini da hawan jini. Bayan tsawon lokaci, hakan kan lalata magudanar jini kuma ya kan ƙara haɗarin toshewar magudanar jini, wanda ya kan haifar da shan inna da bugun zuciya. Duk da haka ana bukatar ƙarin bincike don tabbatar da hakan, kuma illolin lokacin cin abinci a kan lafiyar mutane ba su kai na cin abinci maras kyau ba.
Masu binciken na Faransa sun yi bayani da cewa, a yau, mutane suna kasancewa cikin gaggawa a rayuwar yau da kullum, ba su da isasshen lokaci, wasu da yawa suna cin abincin dare da yamma har ma a dare, wanda ka iya haifar da mummunar tasiri ga lafiyarsu.
Wani bincike da aka yi a baya ya gano cewa, idan tsawon lokacin azumi a dare ya karu, lafiyar mutane tana samun kyautatuwa. Wannan binciken na Faransa ya samar da ƙarin abubuwan shaida ga wannan, wato idan tsawon lokacin azumi a dare ya karu da sa’a daya, haɗarin kamuwa da cututtukan magudanar jini kamar shan inna kan ragu da 7%. Ban da haka kuma, masu binciken sun lura cewa, wadanda suka ci abincin dare da wuri, kashegari kuma suka yi karin kumallo a kan lokaci suna cin gajiya. Wadanda suka ci abincin dare a makare, kashegari suka yi karin kumallo a makare, ko kuma suka tsallake karin kumallo ba sa cin gajiya.
Cututtukan magudanar jini a kwakwalwa suna kan gaba wajen haifar da mutuwar mutane a duk duniya, kuma al’adun cin abinci marasa dacewa suna haifar da matukar hadarin kamuwa da cututtukan magudanar jiki a kwakwalwa. Don haka, cin abincin dare da wuri da yin azumi na tsawon lokaci a daddare na iya taimakawa wajen kare mutane daga kamuwa da cututtukan magudanar jini a kwakwalwa.
