Connect with us

News

Wani Matashi Ya Yi Ajalin Jami’in Vigilante A kano

Published

on

Unguwa gawa
Advertisements
ads

Wani jami’in Vigilante a unguwar Tsamiya da ke Brigade, cikin karamar hukumar Nasarawa a Kano, Idris Salisu, ya rasu bayan da wani matashi da ake zargi, Abubakar Buli, ya caka masa wuka a gefen cikinsa.

Advertisements
Advertisements

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar, inda aka yi gaggawar kai marigayin asibiti, amma ya rasu kafin a kai ga ba shi cikakkiyar kulawa.

Advertisements

Da yake yi wa Hikima Radio karin haske kan faruwar lamarin, Dan uwan marigayin, Haruna Salisu (Dan Jummai), ya ce sun samu labarin rasuwar Idris ne tsakanin ƙarfe 11:30 zuwa 12:00 na rana. Ya ce lamarin ya girgiza su, musamman ganin cewa tashin hankalin ya faru ne cikin lokaci kaɗan.

Advertisements
Advertisements

Kwamandan Vigilante na unguwar Tsamiya, Abdullahi Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an yi jana’izar marigayin bisa ka’idojin addinin Musulunci. Ya ce suna gudanar da aiki tare da jami’an tsaro domin tabbatar da an cafke wanda ake zargi da aikata laifin.

Ya kara da cewa rundunar Vigilante za ta ci gaba da kai rahoton duk wani bayani da zai taimaka wajen gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending