Connect with us

News

Dakarun Sojin Sama Sun Tarwatsa Babbar Mafakar Ƴan Ta’adda, Sun Hallaka Da Dama A Zamfara

Published

on

Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto 
Advertisements
ads

Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta bayyana cewa tawagar jiragen yakin Operation FANSAR YAMMA ta yi nasarar lalata wata babbar mafakar ƴan ta’adda a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, inda aka hallaka da dama daga cikinsu.

A cikin sanarwa da mai magana da yawun NAF, Ehimen Ejodame, ya fitar, an bayyana cewa harin ya gudana ne a ranar 14 ga Nuwamba 2025, bayan cikakken bincike da sa ido da ya tabbatar da cewa yan ta’addan na amfani da sansanin Sauri a matsayin wurin ɓoye shanun da suka sace, da wurin ɓuya daga rundunonin tsaro, da kuma wajen adana kayan aikinsu.

Dakarun Sojin Sama Sun Tarwatsa Babbar Mafakar Ƴan Ta’adda, Sun Hallaka Da Dama A Zamfara

Ejodame ya ce, “Bayan samun ingantaccen bayanan sirri, jiragenmu sun kai hare-hare a matakai da dama kan wuraren da aka tabbatar da kasancewar ƴan ta’addan. Harin ya tarwatsa waɗanda suka tsira, wadanda suka yi yunƙurin gudu cikin dajin da ke kusa.”

Ya ƙara da cewa rundunar ta ci gaba da bin diddigin waɗanda suka tsere, har sai da aka fatattake su gaba ɗaya. An samu nasarar hallaka da dama daga cikin ƴan ta’addan, tare da rushe muhimman gine-gine da wuraren adana kayayyakin da suke amfani da su, wanda hakan ya raunana ƙarfinsu a yankin.

Ejodame ya jaddada cewa Operation FANSAR YAMMA na ci gaba da tabbatar da cewa ƴan ta’adda ba su da mafaka a Zamfara da sauran yankin Arewa maso Yamma, domin dawo da zaman lafiya mai dorewa ga al’umma.

 

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending