News
Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Soke Hukuncin Rijistar Jam’iyyar NDC
Advertisements

Babbar kotun tarayya da ke Lokoja ta soke hukuncinta na baya wanda ya umarci INEC ta yi wa NDC rijista a matsayin jam’iyyar siyasa.
Advertisements
Advertisements
Kotun ta bayyana cewa hukuncin ya shafi haƙƙin Peace Movement Party (PMP), wadda ta yi ikirarin cewa tambarin (logo) da aka yi amfani da shi wajen neman rijistar NDC nata ne, duk da cewa ba a shigar da ita cikin shari’ar ba.
Advertisements
An Daure Auren ‘Yar Farfesa Garba Sambo A Kano, An Yi Wa Ma’auratan Fatan Alheri
Advertisements
Advertisements
Saboda haka, kotun ta umarci a mayar da komai yadda yake kafin hukuncin ranar 10 ga Disamba, 2025, tare da umarnin a haɗa dukkan waɗanda abin ya shafa kafin a sake sauraron shari’ar.
Wannan na nufin duk matakan da INEC ta ɗauka na amincewa da rijistar NDC sun tsaya har sai an yanke hukunci na ƙarshe.
Advertisements
