News
Yadda Siyasa Ke Mayar da Matasan Kano ‘Yan Daba
Daba a harkokin siyasa ta dade tana zama wata babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro a Jihar Kano, inda ake yawan amfani da matasa a lokutan gangamin siyasa, abin da sau da dama ke haddasa tashin hankali da firgici a tsakanin al’umma.
Bincike ya nuna cewa a kusan duk wani taron siyasa a fadin jihar, ana ganin gungun matasa masu dauke da makamai ko kuma wadanda ake zargin suna karkashin tasirin miyagun kwayoyi.
Wadannan matasa kan yi arangama da juna, su kai hari ga jama’a marasa laifi, tare da lalata dukiyoyi — lamarin da ke mayar da harkokin dimokuradiyya zuwa wata hanya ta tada zaune tsaye.
A kasuwar Farm Centre da ke Kano ya sake fito da wannan matsala fili, inda wasu da ake zargi ‘yan daba ne suka kai hari kan ‘yan kasuwa tare da wawushe hajojinsu, abin da ya janyo fargaba a yankin.
Masana sun danganta wannan matsala da tsohon tsarin “’yan banga”, wanda a baya ake amfani da shi wajen kare muradun ‘yan siyasa. Sai dai a yanzu tsarin ya lalace, ya rikide zuwa hanyar amfani da matasa wajen aikata tashin hankali.
Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami’ar Bayero Kano ya bayyana cewa talauci, rashin aikin yi da kuma shaye-shaye na daga cikin manyan dalilan da suka sa matasa suka fada wannan hali.
A cewarsa, “a duk lokacin da aka yi taron siyasa, ana daukar wadannan matasa, a ba su kudi, makamai da miyagun kwayoyi domin su aiwatar da manufofi.”
Ya kuma zargi wasu ‘yan siyasa da nuna munafunci, inda a fili suke Allah-wadai da daba, amma a boye suna cin gajiyarta.
Wani masani, Malam Sulaiman Ahmad, ya ce matsalar daba na da alaka da tabarbarewar tattalin arziki da rashin kyakkyawar alkibla ga matasa.
Ya ce yawancin matasa sun rasa damar inganta rayuwarsu, wanda hakan ke sa su zama kayan aiki ga ‘yan siyasa.
“Idan ana son magance matsala, dole a fara daga tushe, ba daga sama ba,” in ji shi.
A bangaren zamantakewa, Farfesa Abdullahi Maikano Madaki ya jaddada cewa matsalar na da alaka da rashin ingantacciyar tarbiyya da kulawar iyaye.
Ya ce tarbiyyar gida na taka muhimmiyar rawa wajen gina halayen matasa, yana mai gargadin cewa sakaci a wannan fanni na iya haifar da matsaloli masu tsanani a nan gaba.
Rundunar ‘yan sandan Kano ta ce tana daukar matakai domin dakile wannan matsala, tare da jaddada cewa tana aiki tukuru wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
A mahangar Jaridar SolaceBase magance daba a siyasar Kano na bukatar tsari mai zurfi da hadin kai daga dukkan bangarori.
Dole ne ‘yan siyasa su daina amfani da matasa wajen tayar da rikici, su kuma nuna gaskiyar niyyarsu ta kawo karshen wannan dabi’a. Haka kuma, gwamnati ta mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi da ilimi mai inganci.
Iyaye da malamai su kara zage damtse wajen kula da tarbiyyar yara, yayin da shugabannin al’umma za su taka rawar gani wajen wayar da kai.
Idan har ba a dauki matakai masu inganci ba, akwai barazanar cewa daba za ta ci gaba da zama wata cuta mai ci gaba da addabar siyasar Kano da zaman lafiyar al’umma baki daya.
