News
Dr Umar Ardo Zai Maka Jam’iyyar NDC A Gaban Kotu
Wani jigo a ƙungiyar ADA mai neman rajista a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Dr. Umar Ardo, ya yi barazanar gurfanar da jam’iyyar NDC a gaban kotu, bisa zargin karya ƙa’idoji.
Ardo ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan komawar wasu manyan ‘yan siyasa, ciki har da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi, cikin jam’iyyar NDC—lamarin da ya ce ya haifar da tambayoyi kan sahihancin wasu matakai da aka bi.
Jihohin Jigawa, Kano Da Katsina Ne Ke Kan Gaba Wajen Yawan Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta — UNICEF
A wata sanarwa da ya fitar, Ardo ya ce akwai alamun cewa jam’iyyar ta kauce daga tsarin doka da ƙa’idojin siyasa, yana mai cewa hakan ne ya sa ya yanke shawarar neman mafita a kotu domin kare sahihancin tsarin dimokuraɗiyya.
“Ba za mu lamunci take dokoki ba a cikin harkokin siyasa. Dole ne a bi ƙa’ida domin tabbatar da gaskiya da adalci,” in ji Ardo.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jam’iyyar NDC ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da zargin.
Masu bibiyar al’amuran siyasa sun bayyana cewa wannan rikici na iya ƙara tsananta yanayin siyasa a ƙasar, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar sauye-sauyen sheƙar ‘yan siyasa tsakanin jam’iyyu.
-
News7 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News7 days ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Bagwai, Rogo Da Bebeji
