Connect with us

News

Gwamnatin Jigawa Ta Rage Lokutun Aiki Ga Ma’aikatan Jihar Saboda Azumin Ramadan

Published

on

images (3)

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar A. Namadi, ya amince da rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnati a duk faɗin jihar yayin azumin watan Ramadan na shekarar 2026.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban Ma’aikatan Jiha, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya sanya wa hannu, inda ya bayyana sabon tsarin lokutan aiki da za a bi a tsawon watan mai alfarma.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Rufe Mahaƙar Ma’adinai A Filato Bayan Mutuwar Mutum 38

Sanarwar ta ce daga ranar Litinin zuwa Alhamis, ma’aikata za su rika aiki daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana, maimakon ƙarfe 5:00 na yamma da aka saba. A ranakun Juma’a kuwa, za su rufe aiki da ƙarfe 1:00 na rana kamar yadda tsarin ya tanada.

Advertisement

Alhaji Dagaceri ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin sauƙaƙa wa ma’aikata a lokacin azumi, tare da ba su damar samun isasshen lokaci domin shirin buɗa baki da kuma gudanar da ibadu cikin natsuwa.

Ya kuma buƙaci ma’aikatan da su yi amfani da wannan dama wajen ƙara zage dantse a aikinsu, tare da yin addu’o’i domin zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziki a Jihar Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending