Connect with us

News

Akwai Fargabar Rasa Rai Tare Da Jikkatar Su Yayin Rushewar Gini A Jigawa

Published

on

Jigawa building collapse e1757331825389

Mutum ɗaya ya rasu, yayin da wasu bakwai suka jikkata a wani mummunan hatsari na rugujewar gini da aka tattaro cewa ruwan sama ya haddasa, a ƙauyen Kabak da ke ƙaramar hukumar Kirikasamma, jihar Jigawa.

Jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar, Musa Muhammad, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce mutum biyar na kwance a asibiti suna samun kulawa, yayin da aka sallami biyu bayan an yi musu magani.

Advertisement

 

Shugaban ƙaramar hukumar, Muhammad Maji, ya kai ziyarar jaje ga iyalan da abin ya shafa tare da bayar da tallafin kuɗi ga waɗanda suka jikkata da kuma dangin mamacin.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake cigaba da samun rahotannin rushewar gine-gine a sassa daban-daban na ƙasar, musamman manyan biranen Abuja da Legas, abin da ke ƙara janyo damuwa kan ingancin gine-gine a Najeriya.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

TREND NEWS HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending