Connect with us

News

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 23 Tare Da Ceto Mutane 26 A Katsina

Published

on

An yi wata musayar wuta tsakanin sojojin Najeriya da tawagar dan ta'adda Bello Turji

Haɗin gwiwa na rundunar ƙasa da na sama da sojojin sama da ake kira FANSAN YAMMA sun sami nasarar kashe ‘yan bindiga 23 da ceto mutane da akayi garkuwa da su 26 a ƙananan hukumomin Ƙanƙara da Matazu.

Haka kuma bayanai da yake fitowa daga hedkwatar sojoji ta ƙasa, sojojin sun kama wasu ‘yan ta’adda guda 14 a shiyar Arewa maso Gabas da Arewa maso kudu.

Advertisement

Akwai Fargabar Rasa Rai Tare Da Jikkatar Su Yayin Rushewar Gini A Jigawa

Wasu mutane huɗu da ake zargi ‘yan ƙungiyar jihadi ISWAP daga Arewa maso kudu sun miƙa wuya ga sojojin.

Waɗanda sojojin suka ceto sun haɗa da mata 12,yara ƙanana 11 tare da gano baburan hawa guda huɗu da kayan abinci.

Advertisement

Tattaunawa da sojojin suka yi da ‘yan bindigan ya kai su ga maɓoyan ‘yan bindigan a Dutsen Pauwa inda sojojin sukai lugudan wuta har ta kai su ga hallaka ƴan bindigan.

A ƙaramar hukumar Matazu sojojin da suke kai wa da komowa suka sami nasarar kuɓutar da mutane uku a ƙauyen shaiskawa bayan musayar wuta da yan bindigan.

Advertisement

 

 

Advertisement

BLUEPRINT

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending