Connect with us

News

Yadda Iyalai Da Dama Ke Shiga Rayuwar Kufai Bayan Ambaliya Ta Lalata Gidajensu

Published

on

Mutum 259 ne suka mutu yayin da 625,239 suka rasa matsugunansu a ambaliyar ruwa a Nijeriya – NEMA

A duk shekara a Najeriya, musamman a lokacin damina, gidajen marasa galihu ne ke fi rushewa sakamakon ruwan sama, iska ko kuma ambaliya. Wannan matsalar na jefa dubban iyalai cikin tsananin hali, inda da dama daga cikinsu ke rasa matsugunni, lamarin da ya tilasta musu komawa kufai don samun mafaka.

Rahotanni sun nuna cewa ƙarancin gidaje a ƙasar na daga cikin manyan dalilan da ke sa waɗanda suka rasa gidajensu a sakamakon rushewa ko ambaliya, ke zaɓar kufai a matsayin mafaka, duk da hatsarin da hakan ke haifarwa.

Advertisement

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 23 Tare Da Ceto Mutane 26 A Katsina

Masana harkokin muhalli sun ce yawan rushewar gidaje na da alaƙa da gina gine-gine ba bisa ƙa’ida ba, tare da rashin tsari a tsarin birane. Sun ce wannan matsalar ta fi shafar talakawa, musamman a yankunan da ake fama da ambaliya a kai a kai.

Lamarin na faruwa ne a dai-dai lokacin da tattalin arziƙin Najeriya ke ci gaba da fuskantar sauye-sauye da suka jefa miliyoyin ’yan ƙasa cikin ƙuncin rayuwa. Hakan ya haifar da tsananin rashin daidaito a tsakanin al’umma, inda rahotanni na ƙasa da ƙasa ke hasashen ƙaruwa cikin adadin talakawa a ƙasar.

Advertisement

Bayanan tattalin arziƙi na baya-bayan nan sun kuma nuna cewa matsakaita a Najeriya na raguwa sosai, abin da ya bar gibi tsakanin masu ƙarfi da masu rauni kawai. Wannan yanayi na ƙara dagula rayuwar marasa galihu, musamman waɗanda ke rasa matsugunninsu a duk shekara saboda ambaliya.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending