Connect with us

News

Ƙananan Hukumomi 293 A Jihohi 30 Za Su Fuskanci Ambaliya Mai Tsanani A 2025 —Gwamnatin Tarayya 

Published

on

Mutum 259 ne suka mutu yayin da 625,239 suka rasa matsugunansu a ambaliyar ruwa a Nijeriya – NEMA

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jihohi 30 da babban birnin tarayya Abuja za su fuskanci barazanar ambaliya mai tsanani a shekarar 2025, lamarin da zai iya shafar al’ummomi 1,249 a faɗin ƙasar.

Wannan gargaɗin ya fito ne daga Hukumar Kula da Kogi da Tafki ta Ƙasa (NIHSA) a ranar Alhamis yayin ƙaddamar da hasashen ambaliya na shekara ta 2025 a Abuja.

Advertisement

Matatar Ɗangote Ta Saukar Da Farashin Fetur zuwa N865

Ministan Ruwa da Tsabtace Muhalli, Joseph Utsev, ya ce ambaliya na daga cikin manyan bala’o’in da suka fi shafar al’umma a Najeriya, yana mai nuna damuwa kan yadda sauyin yanayi ke ƙara tsananta faruwar ambaliya a ƙasar.

“Mun gano cewa akwai al’ummomi 1,249 a cikin jihohi 30 da babban birnin tarayya da ke fuskantar haɗarin ambaliya mai tsanani. Haka zalika, al’ummomi 2,187 da ke cikin ƙananan hukumomi 293 su ma na fuskantar barazanar ambaliya a matsakaicin mataki,” in ji shi.

Advertisement

Jihohin da ke cikin haɗarin sun haɗa da Abia, Benue, Lagos, Bayelsa, Rivers da Jigawa.

A wani mataki na dakile illar ambaliya, an ƙaddamar da wani sabon tsari na hasashen ambaliya wanda zai bai wa gwamnoni da shugabannin ƙananan hukumomi damar shiryawa da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyi.

Advertisement

Hukumar NIHSA ta roƙi gwamnatocin jihohi da su ɗauki matakan gaggawa domin rage haɗarin da ambaliya ka iya haifarwa, musamman a lokutan damina masu zuwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending