News
Gwamnatin Tarrayya Ta Ayyana Juma’a A Matsayin Ranar Hutu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu ga jama’a domin tunawa da shekaru 27 da Najeriya ta yi tana gudanar da tsarin mulkin dimokuraɗiyya ba tare da tsangwama ba.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babbar Sakatare a Ma’aikatar Cikin Gida, Magdalene Ajani ta fitar ranar Alhamis a Abuja.
An Yabi Bala Wunti a Matsayin Jami’in Gwamnati Mai Nasara da Kishin Jama’a
Ajani ta bayyana cewa Ministan Cikin Gida, Dokta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya amince da wannan sanarwar a madadin gwamnatin tarayya.
Tunji-Ojo ya sake jaddada ƙudurin gwamnatin tarayya na kiyaye martabar dimokuraɗiyya, bin doka da gaskiya, riƙon amana da kuma shugabanci na kowa da kowa.
Ya ba da tabbacin cewa ma’aikatar, tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro da abin ya shafa, za su ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace wajen wargajewa da kuma ƙarfafa tsaron cikin gida na Najeriya.
Ministan ya bayyana cewa, samar da yanayi mai tsaro da kwanciyar hankali yana da muhimmanci ga dimokuraɗiyya da ci gaban ƙasa. Ya buƙaci ’yan Najeriya da su kalli wannan hutu a matsayin wata dama ta yin ɗimbin kishin ƙasa.
“Yayin da muke bikin wannan rana ta tarihi, ana ƙarfafa gwiwar kowane ɗan Najeriya da ya ci gaba da kasancewa mai bin doka, ya mutunta hukumomin da ke ɗorewar dimokuraɗiyyarmu, kuma ya tuna cewa ƙarfin kowace dimokuraɗiyya a ƙarshe ya dogara ne a kan halayyar ‘yan ƙasarta,” in ji shi.
Haka kuma ya bayyana cewa ranar 12 ga watan Yuni na kowace shekara ta kasance rana mai muhimmanci a tarihin Najeriya domin girmama jajircewa, juriya, da sadaukarwar ’yan Najeriya waɗanda ƙoƙarinsu ya sa aka samu gudanar da mulkin dimokuraɗiyya.
