Connect with us

News

‎Ba Gudu Ba Ja Da Baya Wajen Aiwatar Da Dokokin Haraji A Janairun 2026 ‎ ‎— Gwamnatin Tarayya  ‎

Published

on

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta fara aiwatar da sabbin dokokin haraji daga ranar 1 ga watan Janairu, 2026, kamar yadda aka tsara.

‎Ta ce an yi gyaran ne domin bunƙasa tattalin arziƙi da rage wa ’yan Najeriya wahalhalu.

‎Taimakon Soji Daga Kasashen Waje Ba Shi Ne Mafita Ta Dindindin Ga  Gakalubalen Tsaron Najeriya Ba ‎ ‎—SHEHU SANI

‎Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Manufofin Kuɗi da Gyaran Haraji, Taiwo Oyedele ne, ya faɗi haka bayan ya gabatar wa Shugaba Bola Tinubu rahoto a Legas.

Advertisement

‎Ya ce an riga an fara aiwatar da dokoki biyu daga cikin huɗu, yayin da sauran biyun za su fara aiki a watan Janairu.

‎“Shirin fara aiwatar da sabbin dokokin haraji daga ranar 1 ga watan Janairu, 2026 zai tabbata kamar yadda aka tsara,” in ji Oyedele.

‎“Waɗannan gyare-gyare an yi su ne domin samar wa ’yan Najeriya sauƙi.”

‎Oyedele, ya bayyana cewa gwamnati ta shafe watanni tana shirin fara aiwatar da dokokin ta hanyar horaswa, tsare-tsare da wayar da kan jama’a.

Advertisement

‎Ya ƙara da cewa manufar gyaran ba wai tara kuɗi ba ne.

‎“Wannan gyara na nufin bunƙasa tattalin arziƙi da tabbatar da adalci,” in ji shi.

‎“Idan mutane da dama sun shiga tsarin biyan haraji, bin doka zai ƙaru kuma kowa zai amfana.”

‎Gwamnatin ta kuma ce a shirye ta ke ta yi aiki tare da Majalisar Dokoki kan duk wata matsala da ta shafi sabbin dokokin

Advertisement

 

 

AMINIYA

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *