News
Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Kafafen Yaɗa Labarai Kan Tallata ’Yan Ta’adda
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bukaci kafafen yaɗa labarai da su daina tallata ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga da sauran miyagu da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasa.
Ministan ya yi wannan gargaɗi ne ranar Laraba a lokacin da yake jawabi a zama na bakwai na jerin Zauren Bayanai na Ministoci na shekarar 2025, wanda aka gudanar a Cibiyar Yaɗa Labarai ta Ƙasa da ke Abuja.
Annobar Cutar Tumatir Ta Haddasa Asarar Naira biliyan 1.3 A Arewacin Najeriya
Ya ce kafafen yaɗa labarai na da rawar da za su taka wajen gina ƙasa, ta hanyar ƙarfafa gwiwar jami’an tsaro da kuma haskaka nasarorin da suke samu a fagen yaki da ta’addanci.
> “Dole ne mu daina bai wa waɗanda ke aikata ta’addanci muhimmanci. Kada mu ba su gurbin sahun gaba a jaridu ko labarai. Su masu laifi ne, ba su da wata ’yanci da za su kare,” in ji shi.
Ya ce wasu daga cikin waɗannan ’yan ta’adda da miyagu na amfani da kafafen yaɗa labarai da na sada zumunta domin yaɗa fargaba, ƙarya da farfaganda don jan hankalin mutane.
Saboda haka, ya buƙaci ’yan jarida da editoci da su riƙa taka tsantsan wajen bayar da rahoto, su guji manyan kanun labarai masu tayar da hankali da kuma kin zama hanyar tallata farfaganda.
Ministan ya ce, “Waɗannan ba mayaƙan neman ’yanci ba ne. Su masu kisa ne, masu sace mutane ne, masu tada zaune tsaye ne, kuma dole ne a nuna su haka.”
Ya ƙara da cewa inganta tsaro na ɗaya daga cikin muhimman manufofi na Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya haɗa da samar da kayan aiki na zamani ga jami’an tsaro da ƙarfafa binciken leƙen asiri.
Har ila yau, Ministan ya ce Jerin Zauren Bayanai na Ministoci wani dandali ne da ma’aikatarsa ta ƙirƙira domin bai wa ministoci damar bayyana wa ’yan ƙasa nasarorin da suke samu da tsare-tsaren da ake shiryawa nan gaba.
“Muna amfani da wannan dandali wajen sadarwa da ’yan ƙasa kai tsaye ta talabijin da kafafen sada zumunta, domin tabbatar da gaskiya da ɗaukar nauyi,” in ji shi.
Alhaji Idris ya kuma yaba wa kafafen yaɗa labarai bisa rawar da suke takawa wajen wayar da kan jama’a game da ayyukan gwamnati.
A taron, Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar da Ministan Muhalli, Alhaji Balarabe Abbas, sun gabatar da rahotanni kan ayyukan da ma’aikatunsu ke gudanarwa da kuma irin nasarorin da aka samu.
