News
An Hana Binne Gawa A Kano Saboda Rashin Zama ’Yar Unguwa
Wasu ’yan uwa da makusantan wata mamaciyar da ta rasu a Kano sun bayyana takaici da damuwa bayan da wani mai unguwa a unguwar Dan Maliki, Mallam Sulaiman Da’u, ya hana binne gawar mamaciyar a makabartar unguwar, bisa dalilin cewa ba ’yar unguwar ba ce.
Wani daga cikin ’yan uwan mamaciyar ya shaida wa Dala FM Kano cewa, “Abin da Mai Unguwa ya yi mana ya girgiza mu. Ba mu kai gawar unguwar ba sai da makabartar unguwarmu ta cika, kuma dukanmu Musulmai ne.”
Karancin Ruwa: Akwai Gibi Na Lita Miliyan 200 Da Har Yanzu Ba A Magance Ba — Gwamnatin Kano
Wata mata da ke zaune a unguwar Mai Dille ita ma ta koka kan yadda suke fama da matsalar makabarta. Ta roki gwamnati da ta taimaka musu da samar da sabuwar makabarta domin rage wahalhalun da suke fuskanta wajen binne gawarwaki.
Da aka tuntubi Mai Unguwar Dan Maliki, Mallam Sulaiman Da’u, domin jin ta bakinsa. Ya ce al’ummar unguwar ce da kanta ta kafa doka cewa makabartar na gare su ne kawai. Ya kara da cewa doka ce aka fara aiwatarwa a yanzu.
A nasa bangaren, Daraktan kungiyar kare hakkin dan Adam ta Universal Declaration of Human Rights, Kwamared Umar Sani Galadanci, ya ce lamarin na bukatar gwamnati ta shigo ciki. Ya ce “Idan ana maganar hakkoki, dole gwamnati ta saka baki. Dole a samar da mafita domin ba za a ci gaba da barin mutane cikin halin damuwa ba.”
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a ke ci gaba da kiran gwamnati da ta samar da sabbin makabartu a Kano, ganin cewa mafi yawan tsofaffin makabartun da ke cikin birnin sun cika.
