Connect with us

News

Karancin Ruwa: Akwai Gibi Na Lita Miliyan 200 Da Har Yanzu Ba A Magance Ba — Gwamnatin Kano

Published

on

Yan ga ruwa

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa har yanzu akwai gibi na lita miliyan 200 na ruwa da ba a magance ba, duk da gyare-gyaren da ake ci gaba da yi a bangaren samar da ruwa.

Kwamishinan Ruwa na jihar, Injiniya Haruna Doguwa, ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan halin da ake ciki a fannin samar da ruwa ga al’ummar jihar  kamar yanda Jaridar The Independent Mirror ta ruwaito.

Advertisement

Wasu Fusatattu Matasa Sun Kona Alkalin Wasan Ƙwallon ƙafa A Gaban Jama’a

Ya ce ko da an kammala gyaran cibiyoyin Wudil da Joda, da ake sa ran za su kara samar da ruwan daga lita miliyan 300 zuwa miliyan 500 a kullum, har yanzu hakan ba zai iya cike gibin bukatar ruwan da ake da shi ba.

“Jihar Kano na bukatar akalla lita miliyan 700 na ruwa a kullum, amma abin da ake iya samu yanzu bai wuce miliyan 300 ba. Idan aka kammala gyare-gyaren nan, za mu iya kai miliyan 500, amma akwai gibi na miliyan 200 da ba a cika ba,” in ji shi.

Advertisement

Kwamishinan ya ce wannan na nufin cewa wasu sassan jihar za su ci gaba da fama da matsanancin karancin ruwa, musamman a lokacin rani.

A yanzu haka, akwai unguwanni da dama da jama’a ke kwana suna neman ruwa, wasu kuma sai sun saye da tsada, wanda hakan ke kara jefa su cikin mawuyacin hali.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending