News
Zulum Ya Haramta Siyar Da Giya A Borno
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya haramta siyar da giya da sauran kayan maye a birnin Maiduguri da kewaye, yana mai zargin wasu jami’an tsaro da hannu wajen lalacewar tarbiyyar matasa da yaduwar laifuka.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata, yayin kaddamar da kwamitin da zai rushe otal-otal, gidajen karuwai da wuraren da ake zargin ’yan daba da masu aikata laifuka na fakewa a ciki.
Pakistan Ta Harbo Jiragen Yakin India Biyar, Ta Kama Sojoji Takwas
Zulum ya ce jami’an tsaro, ciki har da tsofaffi da ma’aikatan da ke aiki a yanzu, na da rawar da suka taka wajen fadada harkar laifi a jihar, musamman tsakanin matasa.
“Yawaitar siyar da giya da shaye-shaye na haifar da rikici tsakanin kungiyoyi, ya kara karfafa ayyukan kawalci da satar mutane, kuma hakan na barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar,” inji Gwamna Zulum.
Ya ce gwamnatin sa ba za ta ci gaba da zura ido ba yayin da wasu ke ci gaba da cutar da al’umma, musamman matasa da ke fada tarkon miyagun laifuka.
Ya kuma sha alwashin daukar matakan gaggawa don dakile duk wani abu da zai tayar da hankalin jama’a ko bata tarbiyyar al’umma.
