Business
Annobar Cutar Tumatir Ta Haddasa Asarar Naira biliyan 1.3 A Arewacin Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa manoman tumatir a jihohin Kano, Katsina da Kaduna sun tafka hasarar fiye da Naira biliyan 1.3 sakamakon wata cuta da ta kama amfanin gonarsu cikin sa’o’i kaɗan.
Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wani taron horar da bankuna da aka gudanar a Abuja, wanda ƙungiyoyin HortiNigeria da NIRSAL suka shirya.
Ya ce annobar da aka fi sani da Ebola ta Tumatir ta mamaye gonaki a cikin awa 48, inda ta hallaka dubban ton na tumatir. Wannan ya haddasa tashin gwauron zabin farashin kayan lambu a kasuwanni, inda kwandon tumatir ɗaya (kilo 50) ya tashi daga Naira 5,000 zuwa kusan Naira 30,000.
Ministan ya bayyana cewa wannan matsala ta fito da raunin da ke akwai a tsarin noman kayan lambu a Najeriya, musamman rashin isassun kuɗaɗe da dabarun yaƙi da ƙwari da cututtuka.
“Tumatir da barkono na daga cikin muhimman kayan abinci da ake amfani da su a ko’ina a ƙasar nan. Sauyin farashinsu na da tasiri kai tsaye ga rayuwar talakawa,” in ji Kyari.
Ya ƙara da cewa fannin noman kayan lambu na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ayyukan yi, bunƙasa tattalin arziki da fitar da kaya zuwa ƙasashen waje. Ministan ya bukaci a mayar da hankali wajen tallafawa manoman kayan lambu domin rage hauhawar farashin abinci da kuma inganta lafiyar al’umma.