Uncategorized
TSARO: Ba Kasafai Ake Samun Irin Tallafin Da Gwamna Lawal Ke Bawa Sojoji Ba — Babban Hafsan Tsaro
Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya yaba da irin gagarumin goyon bayan da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ke bai wa rundunar Operation Fansan Yamma, yana mai cewa irin wannan tallafi ba kasafai ake samun irinsa ba a ƙasar.
Janar Oluyede ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki da ya kai Jihar Zamfara State, inda ya gana da gwamnan tare da duba hedikwatar rundunar Operation Fansan Yamma da ke Gusau.
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Direban Bas, Sun Yi Awon Gaba Da Fasinjoji A Hanyar Benin Zuwa Lagos
A yayin ziyarar girmamawa da ya kai gidan gwamnatin jihar, Babban Hafsan Tsaron ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin gwamnatin jiha da rundunar sojoji wajen magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin Arewa maso Yamma.
Ya ce ziyarar na da nufin nuna godiya ga gwamnan bisa rawar da yake takawa wajen tallafa wa rundunar, yana mai ƙara da cewa haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen shawo kan ƙalubalen tsaro.
Haka kuma, ya yaba wa al’ummar jihar bisa yadda suke bai wa jami’an tsaro haɗin kai, yana mai jaddada cewa Nijeriya ƙasa ɗaya ce da ke buƙatar haɗin kan kowa domin tinkarar barazanar tsaro.
Janar Oluyede ya ƙara da cewa ya ziyarci hedikwatar rundunar Operation Fansan Yamma, inda ya gana da jami’an tsaro, ya saurari ƙalubalen da suke fuskanta tare da warware wasu daga cikinsu, yayin da aka ɗauki matakan da suka dace kan sauran domin magance su nan gaba.
A nasa ɓangaren, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa magance matsalar ‘yan bindiga a Zamfara na nufin an rage kusan kashi 75 cikin 100 na matsalar tsaro a faɗin Nijeriya baki ɗaya.
Ya ce wajibi ne shugabanni su ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, yana mai jaddada cewa babu wani ƙarfi da ya fi na rundunar sojojin Nijeriya.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa na ci gaba da bayar da cikakken goyon baya ga jami’an tsaro, yana mai tunatar da cewa a baya-bayan nan Ministan Tsaro ya ƙaddamar da sabbin motocin aiki na zamani da gwamnatin jihar ta samar domin ƙarfafa ayyukan rundunar.
Ya ƙara da cewa babu wani ci gaba mai ma’ana da za a iya samu idan babu tsaro, don haka ne gwamnatinsa ke bai wa bangaren tsaro fifiko a cikin manufofinta.
Gwamna Lawal ya gode wa Shugaban Ƙasa bisa tallafin da yake bai wa jihar, tare da jaddada buƙatar ƙarin goyon baya domin samun nasara a yaƙi da matsalar tsaro.
A ƙarshe, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen matsalar ‘yan bindiga a jihar.
