News
An Haramta Wa ‘Yan Kabilar Igbo Nadin Sarautar Gargajiya A Kasashen Waje
An haramta wa ‘yan ƙabilar Igbo nada muƙaman sarautar “gargajiya” a wajen Nijeriya.
Matakin hakan ya biyo bayan takaddamar da ta barke kwanan nan kan nadin “Sarkin Igbo” a ƙasar Afirka ta Kudu, wanda ya haifar da tashin hankali a tsakanin ‘yan Afirka ta Kudu.
TSARO: Ba Kasafai Ake Samun Irin Tallafin Da Gwamna Lawal Ke Bawa Sojoji Ba — Babban Hafsan Tsaro
Yanzu haka ƙungiyar al’adu da zamantakewa ta al’ummar ƙabilar Igbo a faɗin duniya, Ohaneze Ndigbo ta sanar da matakin haramta duk wani naɗi na sarauta a ƙasashen waje, Matakin da gwamnatin Nijeriya ta goyi baya.
Advertisements
