Connect with us

Sports

Gwamnatin Kano Ta Ɗauki Nauyin Horar Da Marubuta Labaran Wassanni 10

Published

on

IMG 20260311 WA0015

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ɗaukar nauyin horar da ’yan jaridar wasanni guda goma domin su yi karatun difloma a fannin Sports Journalism ta wani shiri na ƙasa da ƙasa da ake gudanarwa ta yanar gizo.

Sanarwar ta fito ne daga Ofishin Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ta hannun Ofishin Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Matasa da Wasanni, Sani Musa Danja.

Advertisement

Jami’an NDLEA Sun Kama Mutane 56, Ta Tarwatsa Wuraren Sayar Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano 

A cewar sanarwar, shirin horon na da nufin ƙara wa ’yan jaridar wasanni ƙwarewa tare da basu takardun shaidar da ake buƙata a matakin ƙasa da ƙasa, domin su samu damar shiga manyan ayyukan wasanni na duniya, musamman waɗanda ke ƙarƙashin Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA.

Advertisement

Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Matasa da Wasanni, Sani Musa Danja, ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na bunƙasa matasa da kuma inganta harkokin wasanni a Jihar Kano.

Ya ƙara da cewa horon zai taimaka wajen ƙara inganta yadda ake tattarawa da yaɗa labaran wasanni daga jihar Kano zuwa matakin ƙasa da ƙasa.

Advertisement

Ana sa ran fara gudanar da horon ta yanar gizo a watan Afrilu na shekarar 2026.

Sanarwar ta samu sa hannun MD Coker, mataimaki ga mai ba gwamna shawara kan harkokin matasa da wasanni.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending