Connect with us

Business

Kamfanin NNPCL Ya Rufe Matatar Mai Ta Fatakwal

Published

on

Kamfanin NNPCL ya rufe matatar mai ta Fatakwal
Spread the love

Kamfanin Mai na Ƙasa, NNPCL, ya sanar da shirin rufe matatar mai ta Port Harcourt domin gudanar da gyaran injiniya da nazarin dorewar aiki daga 24 ga Mayu, na shekarar 2025.

Wannan gyara da ake shiryawa zai bai wa kamfanin damar yin nazari kan yadda matatar ke aiki da kuma tabbatar da ingantaccen tsari na ɗorawar samar da mai.

‎Jaridar Inda Ranka Ta Taya Babban Editanta Yasir Sani Abdullahi Murnar Cika Shekaru 26 da Haihuwa ‎

A cewar sanarwar da Olufemi Soneye, Jami’in Hulɗa da Jama’a na NNPC ya fitar, kamfanin ya na aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomi masu ruwa da tsaki, musamman hukumar NMDPRA, domin ganin an gudanar da wannan aiki cikin inganci da gaskiya.

Advertisement

> “NNPC Ltd. na nan daram da kudirinta na tabbatar da dorewar tsaron makamashi a Najeriya,” in ji Soneye.

Kamfanin ya ƙara da cewa za a ci gaba da sanar da jama’a halin da ake ciki ta shafukan sadarwarsa na yanar gizo da sauran kafafen watsa labarai

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *