Connect with us

News

‎Jaridar Inda Ranka Ta Taya Babban Editanta Yasir Sani Abdullahi Murnar Cika Shekaru 26 da Haihuwa ‎

Published

on

Kamfanin Yakam Multimedia, masu wallafa Jaridar Inda Ranka, ya taya babban editanta, Malam Yasir Sani Abdullahi, murnar cika shekaru 26 da haihuwa.

‎Sanarwar taya murnar na kunshe ne a cikin wata takarda da shugaban kamfanin, Kabiru Basiru Fulatan, ya sanyawa hannu a ranar Asabar, inda ya bayyana jin dadinsa kan irin gudunmawar da Yasir ke bayarwa tun daga shigarsa cikin gidan jaridar a matsayin mataimaki na musamman, har zuwa yadda ya kai ga zama babban edita.

Advertisement

ASUU Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki

‎A cewar Fulatan, “Yasir Sani Abdullahi ya kasance kwararren dan jarida mai kishin aiki da jajircewa. Muna alfahari da irin ci gaban da ya samu a cikin kankanin lokaci a fagen aikin jarida.”

‎Shugaban kamfanin ya kara da cewa suna fatan Allah ya kara wa Yasir shekaru masu albarka, cike da lafiya da kuma nasara a dukkan al’amuransa, musamman ma a fannin aikin jarida da ya ke gudanarwa da kishin kasa da kwazo.

Advertisement

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending