Connect with us

News

ASUU Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki

Published

on

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta sake jaddada bukatar ta ga Gwamnatin Tarayya da ta cika dukkan sharuddan yarjejeniyar da aka cimma tun a shekarar 2009, tare da gargaɗin cewa gaza yin hakan zai janyo yajin aiki a matakin kasa.

Shugaban ƙungiyarbASUU na kasa, Dakta Chris Piwuna, ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Juma’a, inda ya zargi gwamnatin tarayya da nuna halin ko-in-kula game da al’amuran da suka shafi jami’o’in kasar.

Advertisement

DSP Barau Jibrin: Shekaru Biyu Na Gwagwarmayar Gina Kasa Da Kare Muradun Jama’a

A cewar Dakta Piwuna, akwai muhimman batutuwa guda tara da har yanzu ba a warware su ba, ciki har da tsaikon da ya biyo bayan kokarin sake duba yarjejeniyar tun daga shekarar 2017, da kuma dakatar da albashin malaman da suka shiga yajin aiki a 2022.

Haka kuma ya yi tir da ci gaba da amfani da tsarin biyan albashi na IPPIS, wanda ASUU ke ganin ya sabawa tsarin gudanar da harkokin ilimi na jami’o’i, tare da barazana ga ‘yancin kai da tsarin tafiyar da jami’o’i yadda ya kamata.

Advertisement

Dakta Piwuna ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawuran da ta dauka, ciki har da sakin kudaden farfado da jami’o’i.

“Ko da yake gwamnati ta sha alwashin saka Naira biliyan 150 cikin jami’o’i da kuma daidaita wasu alawus nan da shekarar 2026, har yanzu babu wani abin da ya tabbata a aikace,” in ji shi.

Advertisement

Ya ce malamai a jami’o’in jihohi kamar Jami’ar Jihar Kogi da ta Jihar Legas na fuskantar wariya, tauye hakkoki da kuma rashin tabbas a matsayin aikinsu, abin da ya kara rage musu kwarin gwiwa da jajircewa wajen gudanar da aikin koyarwa.

“Yanzu haka jami’o’inmu sun zama tamkar fili ne da ake fafata siyasa da kuma kare muradun wasu ‘yan kalilan, wanda hakan barazana ce ga makomar ilimi a wannan kasa,” in ji shi.

Advertisement

Shugaban ASUU ya yi kira da a shirya wani babban taron kasa kan harkar ilimi domin duba matsalolin da suka dabaibaye fannin, musamman batun samun kudade, ‘yancin gudanar da aiki da kuma jin dadin malamai.

Ya ce “ilimi shi ne ginshikin kowace kasa. Idan ba mu bai wa ilimi muhimmanci ba, to ba za mu iya cimma ci gaban da muke muradi ba.”

Advertisement

 

 

Advertisement

NAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending