News
An Cafke Matar Da Ake Zargi Da Kashe Jaririn Kishiyarta Da Guba A Kaduna
Rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ta cafke wata mata mai suna Zaliha bisa zargin kashe jaririn kishiyarta dan wata uku da haihuwa, ta hanyar ba shi guba a kauyen Malari da ke karamar hukumar Soba.
A cewar kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, lamarin ya faru ne ranar 13 ga watan Mayu, a gidan da matan ke zaune tare da mijinsu. Ya ce al’amarin ya faru ne lokacin da uwar jaririn, Maryam Ibrahim, ta shiga bandaki, ta bar dansa a waje. Da ta fito, sai ta tarar da kishiyarta tana rike da jaririn, wanda a lokacin kumfa ke fita daga bakinsa, kuma jikinsa ya soma sauya launi.
Kotu Ta Dakatar Da Yunkurin Trump Na Hana Jami’ar Harvard Daukar Daliban Waje
Bayan haka ne aka garzaya da yaron zuwa asibiti, inda aka tabbatar da rasuwarsa kafin a fara ceto shi.
DSP Hassan ya bayyana cewa bayan gudanar da bincike, Zaliha ta amsa laifin da kanta, inda ta bayyana cewa ta ba jaririn wani sinadari mai hadari da ake amfani da shi wajen hakar asid, bisa dalilin kishi da kiyayya.
“Mun gano cewa kanin mijinta, Lawal Muhammad, ne ya siya mata sinadarin bayan ta bayyana masa cewa bata so ganin jaririn a raye,” in ji DSP Hassan.
Ya kara da cewa ana cigaba da zurfafa bincike don kama Lawal Muhammad domin shima a gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin taimaka wa wajen aikata kisan.
Binciken farko na ’yan sanda ya nuna cewa akwai wata matsala ta sabani tsakanin Zaliha da Maryam Ibrahim, wadda ita ce ta haifi jaririn, sai dai daga baya an ce sun sasanta.
To amma a cewar kakakin ’yan sandan, duk da sulhun da aka yi, Zaliha ta ci gaba da rike kishi a zuciyarta har ta kai ga aikata kisan cikin nufin kawar da jaririn kishiyarta.
DSP Hassan ya tabbatar da cewa rundunar ’yan sanda tana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da Zaliha a gaban kotu da zarar an kammala duk wasu shirye-shirye na shari’a.
