News
Kotu Ta Dakatar Da Yunkurin Trump Na Hana Jami’ar Harvard Daukar Daliban Waje
Wata kotu a Amurka ta dakatar da matakin Shugaban Amurka, Donald Trump, na hana Jami’ar Harvard daukar dalibai daga kasashen waje.
Alkalin kotun gunduma, Allison Burroughs, ce ta yanke hukuncin bayan jami’ar ta garzaya kotu tana kalubalantar matakin gwamnatin Trump na dakatar da shirin musayar dalibai daga waje.
FCTA Ta Ƙwace Filin Sakatariyar PDP Da Wasu Filaye 4,793 A Abuja
Harvard ta ce matakin gwamnatin tamkar ramuwar gayya ne saboda jami’ar ta ki goyon bayan wasu manufofin Trump da ake ganin sun nuna wariya ga ‘yan kasashen waje, musamman baki.
Trump ya sha sukar jami’ar bisa kin bin tsarin sa na sa ido kan baki, inda ya zarge ta da zama mafakar masu kyamar Yahudawa.
Har ila yau, ya sha alwashin cire kudaden tallafi daga jami’ar, wanda ya kai dala biliyan tara, da kuma fitar da wani masanin kimiyya daga sashen kiwon lafiyarta.
Harvard na daya daga cikin manyan jami’o’in duniya da suka fi fitar da mutane da suka yi fice a fannoni daban-daban, ciki har da wadanda suka ci kyautar Nobel fiye da sau 160.
Hukuncin kotun ya kawo karshen kokarin Trump na dakile daukar daliban waje a jami’ar da ke da suna a fadin duniya.
