News
Yadda Farashin Tumatir Ya Fara Sauka A Wasu Kasuwannin Jihar Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Farashin tumatir na ci gaba da sauka yayin da sabon tumatir ya fara shiga kasuwanni a sassan Najeriya idan aka kwatanta da kwanakin baya.
Kano na daga cikin wuraren da aka ruwaito cewa farashin ya sauka da fiye da kashi 60 a kasuwanni.
Yawan Kudin Da Gwamnatin Tinubu Ta Bai Wa Kowane Gwamna A Rabin Shekarar 2024.
Sai dai rahotanni na nuni da cewa attaruhu da albasa farashinsu bai sauka sosai ba.
A kwanakin baya farashin kwandon tumatir ya kai fiye da naira 100,000, al’amarin da ya mutune hakura da amfani da shi .
BBC Hausa ta ruwaito cewa a kasuwar ‘Yan Kaba, taa tabbatar da saukar farashin na tumatir sosai.
Sakataren kungiyar masu sayar da kayan miya na jihar Kano, Aliyu Bello Idris ya ce farashin ya sauka idan aka kwatata da tsadarsa a kwanakin baya.
Ya ce dalilin saukar farashin ba ya rasa nasaba da samun kayan miyar da ake yi a kusa, musamman na daminar bana.
Shi kuma wani dillalin albasa, Rabiu Bamfasy , ya ce har yanzu ita farashinta bai sauka ba.
Bayanai na cewa ba a kasuwar ‘Yan Kaba kadai aka samu saukar farashin kayan miyan ba, har da sauran kasuwanni irinsu Sharada da Sabon Gari da kasuwar Birget da kuma kasuwar Rimi.
‘Yan kasuwar sun tabbatar wa BBC cewa nan da mako uku masu zuwa farashin tumatir din zai kara yin kasa sosai, sai dai babban abin takaicin shi ne manoma da ‘yan kasuwa da dama ba su da fasahar sarrafa tumatir din, idan kasuwarsa ta cika.
-
News21 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
