Connect with us

News

Jami’an Tsaro Sun Ceto Yara 15 Da  Aka Sayar A Kudancin Najeriya

Published

on

images (3)

Hukumar tsaron fararen hula ta Najeriya, NSCDC, ta ce ta ceto wasu yara ƙanana 15 da aka yi safarar su tare da sayar da kowannensu kan kuɗi har Naira miliyan biyu.

Kakakin hukumar na ƙasa, Babawale Afolabi, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa an gano yaran ne bayan jami’an hukumar sun gudanar da bincike mai zurfi.

Wani Magajin Gari A Ƙasar Faransa Ya Kafa Dokar Hana Sauro Shawagi A Cikin Garin

Binciken ya nuna cewa wani mutum mai suna Anderson Archibong, wanda ake zargi da yin amfani da sunan ƙungiyar kare haƙƙin yara, ya yaudari iyayen yaran a Jihar Nasarawa.

An ce Archibong ya yi amfani da wani shiri na bogi mai suna “Back to School Project”, inda ya yi wa iyayen alkawarin samar wa ’ya’yansu ilimi kyauta, alhali manufarsa ita ce safarar yaran da sayar da su.

Jami’an tsaron sun yi nasarar gano yaran tare da kuɓutar da su daga jihohin Anambra, Imo da Enugu, inda ake zargin an riga an rarraba su ga masu saye.

Advertisement

 

RFI

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending